Barazana: Tsohon gwamna Yari zai dauki mataki a kan wasu kafofin watsa labarai

Barazana: Tsohon gwamna Yari zai dauki mataki a kan wasu kafofin watsa labarai

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi barazanar daukar mataki da hukunce-hukunce na shari'a a kan wasu kafofin watsa labarai 3 da ke yada rahotanni kamar yadda ya bayyana a matsayin karairayi a kansa.

Barazanar tsohon gwamnan ta zo ne a ranar Alhamis cikin wata sanarwa da ya gabatar a birnin Gusau wadda ta fito daga bakin mai magana da yawunsa, Alhaji Ibrahim Dosara.

Wannan lamari ya biyo bayan simamen da hukumar hana yiwa tattalin arziki ta'annati EFCC ta kai gidansa dake garin Talata Mafara a ranar 4 ga watan Agusta.

Domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, jami'an hukumar EFCC sun kai wani simame na bazata gidan tsohon gwamnan domin gudanar da bincike da ya shafi yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa.

Dosara cikin sanarwar da ya gabatar ba tare da bayyana sunayen kafofin watsa labaran ba, ya yi zargin cewa su na yada rahotanni na shaci fadi da manufa ta bata sunan ubangidansa da kuma shafa masa bakin fyanti.

KARANTA KUMA: Tsaro: Manyan sojojin Amurka 13 na zagaye a Najeriya

Ya buga misali da yadda daya daga cikin kafofin watsa labaran ta yi soki burutsu na bayyana wani rahoto da ke nuni da cewa, jami'an hukumar EFCC sun yi kacibus da motoci 21 na alfarma a gidan tsohon gwamnan yayin gudanar da bincikensu.

Da wannan ne Dosara ya ke shawartar kafofin watsa labaran uku da su gaggauta janye rahotannin karya da suka wallafa a kan tsohon gwamnan cikin sa'a 24 ko kuma lamarin ya kai har gaban kotu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel