Tattalin arziki: Najeriya ba ta da wanda ya fi Buhari - Garba Shehu

Tattalin arziki: Najeriya ba ta da wanda ya fi Buhari - Garba Shehu

A yayin mayar da martani ga babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya PDP, fadar shugaban kasa ta ce ba bu wata mafificiyar mafita da za ta tabbatar da kyakkyawar makoma ga tattalin arzikin kasar nan da ta wuce shugaba Muhammadu Buhari.

Fadar shugaban kasa ta karyata ikirarin jam'iyyar PDP wadda ta ce tattalin arzikin Najeriya na cikin babbar matsala gami da fuskantar tasgaro a yanzu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, wanda ya yi watsi da ikirarin jam'iyyar PDP a wata sanarwa da ya gabatar cikin garin Abuja a ranar Laraba, ya tunatar da jam'iyyar irin kwazon da gwamnatin Buhari ta yi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Mallam Garba yayin tabbatar da sahihancin tarihi ya ce gwamnatin Buhari ta yi hobbasa wajen habakar tattalin arzikin Najeriya tun daga shekarar 2015 kawo yanzu. Ya kuma tunatar da jam'iyyar irin durkushewar da tattalin arzikin kasar ya yi karkashin jagorancinta a shekarar 2014.

KARANTA KUMA: An gano wani gari da aka shafe shekaru 10 ba a haifi namiji ba

Hadimin shugaban kasar ya yi fashin baki dangane da yadda akidar gwamnatin Buhari a wa'adi na farko ta inganta dangartakar harkokin kasuwancin Najeriya da kasar Sin, Amurka da kuma nahiyyar Turai baki daya domin bunkasar tattalin arziki.

Ya kuma buga misali da yadda gwamnatin Buhari ke ci gaba da narkar da makudan kudi wajen inganta ci gaban gine-gine a lokaci guda da ta ke fafutikar tsimi da tanadin kimanin kaso 30 cikin 100 na kasafin kudin kasar nan a kowace shekara.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel