Yanzu Yanzu: DSS ta samu yardar kotu na tsare Sowore har tsawon kwanaki 45

Yanzu Yanzu: DSS ta samu yardar kotu na tsare Sowore har tsawon kwanaki 45

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince wa hukumar yan sandan farin kaya (DSS) da ta tsare Omoyele Sowore na tsawon kwanaki 45.

An kama Sowore a ranar Asabar da ya gabata gabannin zanga-zangar juyin juya hali.

Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, 8 ga watan Agusta, Justis Taiwo Taiwo, yace zai bari hukumar ta tsare Sowore na tsawon kwanaki 45 a karon farko, wanda ana iya sabonta shi idan an nemi hakan, domin ba DSS damar kammala bincikenta.

A karar da DSS ta shigar, karkashin sashi na 27 na dokar hana ta’addanci, hukumar ta zargi Sowore da aikata ta’addanci.

Ta kuma gabatar da faifan bidiyo biyu, wanda ke dauke da rikodin haduwar Sowore da Nnamdi Kanu, Shugaban kungiyar masu fafutukar neman yankin Biyafara da kuma wata hira inda Sowore yace mamboin kungiyar Shi’a ma za su hada hannu da shi wajen durkusar da gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Buhari da APC sun yi garkuwa da yan Najeriya - PDP

A wani labari na daban mun ji cewa jami’an hukumar DSS masu fararen kaya a jihar Edo sun kama wasu mutum biyu da a ke zargi da yin shiga a matsayin Mai dakin shugaban kasan Najeriya watau Hajiya Aisha Buhari.

Haka zalika kuma an kama wani mutumi da ke amfani da sunan mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo.

Mun samu wannan labari ne a Ranar 7 ga Watan Agusta, 2019. Mataimakin Darektan hukumar na DSS a Edo, Galadima Byange, shi ne ya gabatar da wadannan wadanda a ke zargi da laifi masu suna Amos Asuelimen da Kelvin Ogashi a Garin Benin jiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel