Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban INEC, Farfesa Maurice Iwu ya isa kotu

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban INEC, Farfesa Maurice Iwu ya isa kotu

Tsohon shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Maurice Iwu ya iso Kotun Tarayya da ke Legas domin gurfana gaban alkali.

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) ta ce za ta gurfanar da Iwu bisa tuhumar da ake masa na damfara ta naira biliyan 1.2.

Za a gurfanar da Farfesa Iwu a kotu bisa tuhumarsa da aikata laifuka hudu masa alaka da karkatar da kudin gwamnati a cewar EFCC.

DUBA WANNAN: Cin amana: Nayi nadamar kyalle mata ta shiga siyasa - Wani magidanci ya fada wa kotu

Anyi ikirarin cewa tsakanin watan Disamban 2014 zuwa Maris din 2015, Iwu ya boye Naira biliyan 1.2 a asusun ajiyar banki na Bioresources Institute of Nigeria Limited da ke bankin United Bank for Africa Plc da aka fi sani da UBA.

EFCC tayi zargin kudin na cikin Naira Biliyan 23.29 da tsohuwar ministan albarkarun man fetur, Diezani Allison Madueke ta ba shi ne domin tafka magudi a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

EFCC tayi Iwu yana daya daga cikin wadanda suka amfan da wannan kudin ciki har da wasu jami'an INEC da a halin yanzu suke fuskantar tuhume-tuhume danban-daban a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel