Gwamnoni sun dau alkawarin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Gwamnoni sun dau alkawarin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

-Gwamnonin Najeriya za su hada hannu da Bankin Afirka domin tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

-Mun samu wannan labarin ne a sakamakon wata ganawa da ta gudana tsakanin NGF da AFDB a babban birnin tarayya Abuja

-Mataimakin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ne ya jagoranci zaman

Gwamnonin jihohin Najeriya talatin da shida sun gana da jami’an Bankin cigaban Afirka wato AFDB a Abuja, inda suka tattauna hanyar da za a bi domin tsamo ‘yan Najerya sama da miliyan hamsin daga talauci ta hanyar sanya jari a cikin harkar noma.

Shugaban kula da lamuran labarai na Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF, Abdulrazak Bello Barkindo ya ce, taron ya ta’allaka ne a kan bude kamfanonin sarrafa kayayyakin gona a sassa daban-daban dake kasar nan.

KU KARANTA:Tsige mataimakin gwamna: Maganar cewa zan sauya sheka karyar banza ce – Achuba

A wani zancen da Barkindo ya fitar, ya bayyana mana cewa an gudanar da taron cikin tsanaki a tsakanin NGF wadda mataimakin shugaban kungiyar Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, yayin da AFDB ya samu wakilicin Farfesa Oyebanji Oyeyinka.

Barkindo ya ce: “ Tattaunawar ta mayar da hankali ne a kan harkokin noma da yadda za ayi amfani da noman domin cin amfanin albarkatun gonan da Allah ya bai wa Najeriya wadanda manoma ke samarwa ta ko wane hali.”

Har ila yau, an aminta da cire makudan kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan daya ($1bn) domin zuba jari a wannan shiri cikin shekaru uku. Ana tsammanin sa hannun kungiyoyi kamar su NIRSAL da NIPC cikin shirin.

Manufar taron dai duk bata wuce zakulo bangaren da gwamnonin za su iya bayar da tasu gudunmuwa ba domin cigaban al’ummarsu a fagen noma.

Mataimakin kungiyar gwamnonin Najeriya Aminu Waziri ya ce: “ Dukkkanin jihohin Najeriya 36 za su dubi wannan shiri domin bunkasa samar da ayyuka yi da kuma rage talauci musamman a tsakanin matasanmu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel