Kungiyoyin arewa sun nemi Buhari ya ba yan Najeriya hakuri

Kungiyoyin arewa sun nemi Buhari ya ba yan Najeriya hakuri

Hadakar kungiyoyin Arewa a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba al'umman kasar hakuri bisa zargin jefa kasar cikin matsananciyar yanayi.

Kungiyar a wani jawabi da kakakinta, Abdul-Azeez Suleiman ya gabatar, ya ci gaba da bukatar shugaban kasar da ya karbi laifin gazawa sannan kuma ya dauki matakan magance matsalolin kasar.

Tace ko da yake yankin Arewa na sane da tangardan da gwamnatin wadanda suka zama abun damuwa, yan Arewa sun yanke shawarar kin shiga zanga-zangar juyin juya hali ba, saboda yarda da suke da shi cewa ana iya warware duk wani lamari da ya shafi rashin jituwa ba tare da tashin hankali ba.

Kungiyar tace tana sane da kalubale da dama da kasar ke fuskanta a kasar a karkashin gwamnatin Buhari kamar ta’addancin, kungiyar Boko Haram, rikicin manoma da makiyaya, tattalin arzikin da bata tafiya, nuna bangarenci wajen nade-naden mukamai, kasafin kudi, yaki da rashawa wanda babu adalci cikinta, da rashin bin doka.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Jerin jihohi 15 da za su fuskanci matsananciyar ambaliyar ruwa

Kungiyar dai har ila yau ta daura ma yankin Kudu masu Yamma laifi, wanda tayi ikirarin cewa sun kasance mafi amfana daga gwamnatin Buhari, sannan kuma kan gaba wajen kaskantar da kokarin gwamnatin.

Ta bukaci yankin Arewa da ta kara dankon dangantaka da yankin kudu maso Gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel