Buhari da APC sun yi garkuwa da yan Najeriya - PDP

Buhari da APC sun yi garkuwa da yan Najeriya - PDP

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyar Peoples Democratic Part (PDP) sun baana cewa a karkashin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC), rashin tsaro da rashin tabbass ga lamarin siyasa ya karu sosai.

“A bayyane ake cewa APC da fadar shugaba Buhari sun yi garkuwa da yan Najeriya."

A cewar wani jawabi daga kakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbodiyan, jam’iyyar tace ta sake duba mawuyacin halin da tattalin arziki da kuma tashe-tashen hankula a dukkanin yankunan kasar sannan hakan ya sa ta ga akwai bukatar jan hankali akan cewa “kasar na durkushewa.”

Jam’iyyar PDP tace ta damu matuka akan halin da kasar ke ciki, wanda damokradiyyarta da yancin al’umma hadi da shugabanci na gari duk ya tabarbare a yanzu, a karkashin shugaba Buhari.

A cewar jam’iyyar wannan hali da kasar ke ciki ya kai har a yanzu al’umman kasar na matukar kokarin ganin sun kwato yanci da makomarsu da kansu.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Jerin jihohi 15 da za su fuskanci matsananciyar ambaliyar ruwa

PDP ta bayyana cewa a yanzu hana tafiyar da yan Najeriya kamar mutanen da aka cinye da yaki, inda tayi korafin cewa a yanzu yan Najeriya basu da ikon gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ta basu yancin yi.

Tace wannan hali da kasar ta tsinci kanta a karkashin mulkin shugaba Buhari ya kasance babban barazana ga al’ummanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel