Tsige mataimakin gwamna: Maganar cewa zan sauya sheka karyar banza ce – Achuba

Tsige mataimakin gwamna: Maganar cewa zan sauya sheka karyar banza ce – Achuba

-Simon Achuba ya karyata batun cewa ya na shirin ficewa daga jam'iyyar APC

-Mataimakin gwamnan ya yi wannan maganar ne matsayin martani bisa ga shirin tsige shi da majalisar jihar Kogi ke yi

-Har yanzu ina nan a jam'iyyata ta APC kuma babu wata alaka tsakanin yinkurin cire ni da kuma sauya jam'iyya inji Achuba

Mataimakin gwamnan Jihar Kogi, Simon Achuba ya watsi da maganganun da ke yawo a yanzu cewa wai zai koma jam’iyyar PDP a matsayin labarin kanzon kurege.

Achuba ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake mayar da martani game da shirin tumbuke shi da Majalisar Dokokin Jihar Kogin ke yi.

KU KARANTA:Eid-el-Kabir: Obaseki ya bada umarnin biyan albashin watan Agusta kai tsaye

Mataimakin gwamnan ya yi wannan maganar tasa ne a gidan talabijin na Channels TV inda aka gayyace shi a matsayin babban bako cikin shirin ‘Siyasar yau’, inda ya ce yinkurin na tumbuke shi ba abin mamaki bane.

Ya kara da cewa, wannan maganar na fitowa ne a sakamakon fallasa asiran gwamnatin jihar da yayi da kuma abinda ke faru na hakika dangane da siyasar Kogi.

Mataimakin gwamnan ya ce maigidansa na amfani ne kawai da karfin majalisa a kansa domin ya kore maganar cin-hanci da rashawa da ta dabaibaye gwamnatinsa kamar yadda aka ambata a baya.

Achuba ya nemi jama’ar jihar Kogi da su kwantar da hankalinsu kana su fita zuwa wurin sana’o’insu saboda a cewarsa ko ba jima ko ba dade gaskiya za tayi halinta.

Da kuma yake karin haske a kan batun cewa ya shirya sauya jam’iyya cewa yayi: “ Wannan maganar karya ce, zance kawai maras tushe balle makama abinda kawai nake so in sanar da jama’a kenan.”

A karshe ya sake jaddada kalamansa ga al’ummar jiharsa cewa har yanzu yana nan a matsayinsa na dan jam’iyyar APC. Babu abinda ya hada barazanar tumbuke shi da sauya jam’iyya kamar yadda ya fadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel