Ambaliyyar ruwa da tayi sanadiyar rasuwar dalibai 4 a ATBU kaddara ne daga Allah - Gwamna Mohammed

Ambaliyyar ruwa da tayi sanadiyar rasuwar dalibai 4 a ATBU kaddara ne daga Allah - Gwamna Mohammed

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ya bukaci daliban Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi (ATBU) su dauki iftila'in da ya faru a jami'ar inda wasu dalibai hudu suka mutu a matsayin kaddara daga Allah.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke tarbar shugabanin Kungiyar Daliban Jihar Bauchi (NUBASS) da suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnatin Bauchi kuma suka bukaci ya bayar da umurnin sake gina gadar da ta rufta tayi sanadin rasuwar dalibai hudu.

Gwamnan da ya samu wakilcin Kakakin Majalisar Jihar, Alhaji Yakubu Sulaiman ya tabbatarwa daliban cewa gwamnati za ta dauki matakin da ya dace don gyara gadan.

DUBA WANNAN: Wata mata tayi yunkurin siyan mota da kudin jabu da ta buga a gidanta

Shugaban NUBASS, Ibrahim Hashimu Abdullahi ya bukaci gwamnatin ta samar wa dalibai asibitoci da famfon tuka-tuka domin rage wahalhalun da daliban ke fuskanta a jami'ar.

Shugaban jami'ar, Farfesa Muhammad Ahmad Abdulazeez ya ce kawo yanzu an tabbatar da rasuwar dalibai uku kuma babu wani dalibi da ya bace.

Ya yi wannan jawabin ne a jiya Laraba yayin da ya gana da wakilin gwamna Bala Muhammad da ya kai masa ziyarar ta'aziyya a jami'ar.

Ya ce mahukunta jami'ar sun kafa muhimmin kwamiti da za ta gano hanyoyin magance afkuwar wani abu mai kama da wannan a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel