Jerin sunaye: Gwamna Matawalle ya nada sabbin sakatarorin kananan hukumomi 14 a Zamfara

Jerin sunaye: Gwamna Matawalle ya nada sabbin sakatarorin kananan hukumomi 14 a Zamfara

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Laraba ya sallami dukkan shugabanin kananan hukumomi 14 a jihar tare da bayar da umurnin nada wadanda za su maye gurbinsu.

Gwamnan ya kuma amince da naddin Shugaban Polyteknic da Kwallejin Ilimi da ke Jihar.

Hakan na cikin wata sanarwar ce mai dauke da sa hannun Direkta-Janar na Harkokin Watsa Labarai na gwamnan, Yusuf Idris a garin Gusau.

Gwamnan ya umurci dukkan sakatarorin da aka sallama su mika takardun ajiye aikinsu a Hukumar Kula Da Ayyukan Kananan Hukumomi da Masarautu.

DUBA WANNAN: Wata mata tayi yunkurin siyan mota da kudin jabu da ta buga a gidanta

Sabbin sakatarorin kananan hukumomin da aka nada sun hada da Abubakar Bakura, Karamar hukumar Bakura; Rabiu Pamo, Karamar hukumar Anka; Abdulkadir Gora, Karamar hukumar Birnin-Magaji; Lawali Zugu, Karamar hukumar Bukkuyum; Sani Mainasara, Karamar hukumar Bungudu, Rabiu Hussaini, Karamar hukumar Gummi and Nura Musa, Karamar hukumar Gusau.

Sauran sun hada da Bashir Bello na Karamar hukumar Kaura-Namoda, Ahmadu Mani, Karamar hukumar Maradun, Salisu Yakubu, Karamar hukumar Maru, Abba Atiku, Karamar hukumar Shinkafi; Ibrahim Garba, Karamar hukumar, Talata-Mafara; Aliyu Lawali, Karamar hukumar Tsafe da Bala Dauran, Karamar hukumar Zurmi.

Har ila yau, sanarwar ta kuma ce an nada Dakta Sha'ayau Mafara a matsayin shugaban Abdu Gusau Polyteknic da ke Talata-Mafara da Muhammad Maradun a matsayin rajistra na makarantar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel