Dakarun ‘Yan Sanda sun kashe Abacha, wani ‘Dan fashi da makami a Ribas

Dakarun ‘Yan Sanda sun kashe Abacha, wani ‘Dan fashi da makami a Ribas

Rahotanni sun same mu cewa wata babbar Rndunar ‘Yan sandan Najeriya sun yi nasarar kashe wani rikakken ‘Dan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane wanda a ke kira Abacha.

Wannan hatsabibin mai laifi shi ne shugaban ‘yan fashin da su ka hana mutanen Yankin Emohua sakat a cikin jihar Ribas. Abacha ya mutu ne a lokacin da ya ke fada da Dakarun ‘yan sandan kasar nan.

A wajen wani gumurzu ne da a ka yi tsakanin wannan ‘dan fashi da ‘yan sandan Najeriya a ka harbe sa da bindiga har lahira. Wannan abu ya faru ne a sansanin Rumuakunde a cikin Garin Emohua.

Kamar yadda manyan jami’an ‘yan sandan jihar Ribas su ka bayyana, Dakarun tsaron sun kai wa manyan fashin hari ne inda su ka yi dace, su ka karbe wasu manyan makamai da Miyagun ke ta’adi da su.

KU KARANTA: DSS sun kama masu damfara da sunan fadar Shugaban kasa

Kakakin ‘yan sandan Ribas, Nnamdi Omoni, ya ce Dakarun kasar na Operation Sting da wata Runduna da ke Garin Rumuji ne su ka kai wannan hari ne a Ranar Laraba, 7 ga Watan Agusta, 2019.

‘Yan sandan sun kai wannan samame ne a lokacin wadannan ‘yan fashi da makami ba su farga ba. “An harbi Abacha ne yayin da ya ke kokarin tserewa a lokacin da a ke gumurzu da Jami’ai” Inji Omoni.

DCP Omoni ya kuma kara da cewa: “Wasu gungun ‘yan fashin sun samu rauni a wannan hari. “Kwanan nan za a gabatar da wadanda a ka kama, daga ciki har da wani shu’umi mai suna Ekueme”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel