Tattalin arziki: Najeriya na cikin matsala bayan mai ya koma $56

Tattalin arziki: Najeriya na cikin matsala bayan mai ya koma $56

Farashin danyen man fetur ya yi kasa a kasuwar Duniya inda yanzu a ke saida kowane gangar danyen man Najeriya a kan Dala 56. Hakan na iya zama barazana ga Najeriya a wannan shekara.

Najeriya ta yi kasafin cewa za ta saida mai a kan Dala 60, sai dai kuma yanzu gangar danyen man kasar bai kai wannan kudi a kasuwa ba. Wannan zai jawo Najeriya ta nemi cikon kudi a 2019.

A Ranar Talatar makon nan, 6 ga Watan Agusta, 2019, gangar danyen mai na Brent ya sauka daga kusan Dala 60 zuwa Dala 56.34. Farashin man bai taba sauka irin haka ba a cikin shekaru bakwai.

Farashin man Najeriya ya karye da 20% daga Afrilu zuwa yanzu. A na ta samun wannan saukar farashi ne yayin da manyan Duniya watau Amurka da kasar Sin su ke ta faman yakin kasuwanci.

KU KARANTA: Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari za ta ceci Najeriya

A kasafin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu wannan shekarar, Najeriya ta na sa ran saida gangunan mai miliyan 2.3 a duk rana a kan akalla Dala 60 ne a kasuwannin Duniya.

Wani babban Masanin harkar man fetur a Duniya, Gene Mc Gillian ya bayyana cewa farashin danyen mai ya tasirantu da rikicin kasuwancin da kasar Amurka ta ke yi da China a halin yanzu.

Duniya za ta zura idanu domin ganin yadda kasuwar za ra kaya a daidai wannan lokaci. Najeriya ta na sa ran samun kudin da za ta iya biyan albashin ma’aikata sannan kuma ta yi wasu ayyukan.

Abin da Amurka ta ke saye na danyen man fetur ya ragu daga ganga miliyan 2.8 a duk rana zuwa ganguna miliyan 2.4. Masanan tattalin arzikin Duniya ba su hararo wannan karyewar farashi ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel