EFCC za ta tasa keyar tsohon shugaban INEC gaban kotu kan satar naira biliyan 1.2

EFCC za ta tasa keyar tsohon shugaban INEC gaban kotu kan satar naira biliyan 1.2

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kammala shirin gurfanar da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mauricu Iwu gaban kotu.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito kaakakin hukumar EFCC, Tony Orilade ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, inda yace hukumar na tuhumar Iwu da satar naira biliyan 1.2.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kai harin kunar baki wake jahar Borno, 3 sun mutu

Sai dai majiyar Legit.ng ya ruwaito kaakaki Orilade bai bayyana ranar da hukumar za ta tasa keyar Iwu gaban kotu ba, amma ya tabbatar da cewa zasu tasa keyarsa gaban babbar kotun tarayya dake Legas ne a kan tuhume tuhume guda hudu da suka danganci satar kudade.

EFCC ta bayyana cewa Farfesa Maurice Iwu ya wawure kimanin naira biliyan 1.2 mallakin Bioresources Institute of Nigeria Limited dake jibge a wani asusun bankin UBA a tsakanin watan Disambar 2014 zuwa watan Maris na 2015.

Idan za’a tuna a watan Yunin 2005 ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya nada Maurice Iwu shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, inda aka cireshi a watan Afrilun shekarar 2010.

An koka da Iwu a zamanin da yake shugabantar INEC sakamakon yawaitan magudin zaben da aka yi a zamaninsa, zaben 2007, inda a wasu jahohi aka sanar da sakamakon zabe tun kafin yan dangwale su kammala dangwale.

A wani labarin kuma, jami’an EFCC sun kama wani basarake a karamar hukumar Gummi ta jahar Zamfara da laifin karkatar da tireloli 3 na takin zamani da gwamnati ta sayo don raba ma manoman shinkafa, inda ya sayar dasu ga wani attajiri a kan kudi naira miliyan 17.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel