Zan rika tunawa da Jam’iyyar APC wajen daukar mataki – Buhari

Zan rika tunawa da Jam’iyyar APC wajen daukar mataki – Buhari

Mun samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da shugabannin jam’iyyarsa ta APC cewa nan gaba zai rika duba abin da jam’iyya ta ke so kafin ya dauki babban mataki.

Shugaban kasar ya ba shugabannin jam’yyar wannan kwarin-gwiwa ne a lokacin da su ka yi wani zama a Ranar Laraba 7 ga Watan Agusta, 2019, a fadar shugaban kasa da ke babban birnin Abuja.

Muhammadu Buhari ya nuna cewa zai ba jam’iyyar girmanta, tare da kuma yabawa irin kokarin da shugaban APC na kasa watau Adams Oshiomhole da mutanensa su ka yi a babban zaben 2019.

Shugaban kasar ya ke cewa: “Ya bayyana a zahiri cewa nasarar jam’iyya ta ke gabanku. Da kun ga dama, da kun yi amfani da lokaci da karfin da ku ka ba APC wajen ganin kun gina kan ku.

KU KARANTA: An kai samame gidan tsohon Gwamnan APC a Najeriya

“Ina girmama kokarin da ku ke yi; a na samun gamsuwa ne kurum idan mutum ya bautawa kasar da kuma jama’anta, domin idan abin Duniya a ke nema, babu wanda zai iya biyanku.” Inji Buhari.

Shugaba Buhari ya fadawa majalisar NWC cewa zai rika zakulo wasu daga cikin ‘Ya ‘yan APC da su ka cancanta domin su rike mukamai a manyan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Shugaban jam’iyya, Adams Oshiomhole, ya taya Buhari murnar nasarar da ya samu tare da nuna farin cikin karbe jihohin Kwara da Gombe, sai dai ya kuma yi takaicin wasu jihohi da APC ta rasa.

“A Kwara mun tunbuke gidan da ke mulki, mu ka kafa wadanda ke yi wa jam’iyyar APC biyayya a gwamnati.” Oshiomhole ya ce wannan ne zaman farko da majalisar NWC ta yi da Buhari bayan zabe.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel