DSS sun cafke masu damfara da sunan Aisha Buhari da Osinbajo a Facebook da Instagram

DSS sun cafke masu damfara da sunan Aisha Buhari da Osinbajo a Facebook da Instagram

Mun ji cewa jami’an hukumar DSS masu fararen kaya a jihar Edo sun kama wasu mutum biyu da a ke zargi da yin shiga a matsayin Mai dakin shugaban kasan Najeriya watau Hajiya Aisha Buhari.

Haka zalika kuma an kama wani mutumi da ke amfani da sunan mataimakin shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo. Mun samu wannan labari ne a Ranar 7 ga Watan Agusta, 2019.

Mataimakin Darektan hukumar na DSS a Edo, Galadima Byange, shi ne ya gabatar da wadannan wadanda a ke zargi da laifi masu suna Amos Asuelimen da Kelvin Ogashi a Garin Benin jiya.

Galadima Byange ya ce wadannan masu laifi sun damfari akalla mutane biyar inda su ke neman katin waya da kudi da sunan za a ba su bashin kudi N100, 000 da jari a kafafen sadarwan zamani.

KU KARANTA: EFCC: Shugaban Manoma ya hada kai da Jami’in Gwamnati ya saci taki

DSS ta ce Mista Amos Asuelimen Dalibin kasuwanci ne a jami’ar Ambrose Alli da ke Garin Benin. An yi nasarar damke shi ne a Garin Ubiaja, da ke cikin karamar hukumar Esan a jihar Edo.

Asuelimen da bakinsa ya ke cewa: “Na san abin da ya sa a ka kama ni, na bude shafin Facebook ne da sunan Yemi Osinbajo domin a damfari jama’a. Ina amfani ne da waya ta ta Infinix”

Shi kuma Ogashi ya bude shafin Instagram ne da sunan Mai dakin shugaban kasa watau Hajiya Aisha Buhari inda ya ke yi wa Matasa karyar zai ba su jari. An kama shi ne a Garin Ikpoba-Okha.

Jami’an hukumar DSS sun bayyana cewa nan gaba kadan za a gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu. Jami’an tsaron sun kuma gargadi jama’a da su guji iri wannan mugun aika-aika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel