Ai ga irinta nan: 'Yan sanda sun gurfanar da lauya bayan wanda yake kare wa ya tsere

Ai ga irinta nan: 'Yan sanda sun gurfanar da lauya bayan wanda yake kare wa ya tsere

A ranar Talata ne jami'an 'yan sanda suka gurfanar da wani lauya, Muhammed Ali, mai shekaru 37, a gaban wata kotu mai daraja ta daya dake u guwar Kabusa da ke Abuja, bayan ya gaza gabatar da wani laifi ake tuhuma da aikata ta'addanci.

Ali, mazaunin gida mai lamba 55,321 da ke rukunin gidajen Gwarimpa, ya tsaya wa wani Muazu Omolari, wanda ake zargi da yi wa wata budurwa, Victoria Inaji, barazana.

Dan sanda mai gabatar da kara, Mahmud Lawal, ya sanar da kotu cewa Victoria ce ta kai rahoton Omolari ofishin 'yan sanda na unguwar Garki a ranar 24 ga watan Yuni, bayan ya yi mata barazana.

A cewar Lawal, ana tuhumar Omolari ne sai lauya Ali ya tsaya masa har aka bayar da shi beli bisa sharadin cewa zai gabatar da shi duk lokacin da ake bukatarsa.

DUBA WANNAN: Da sauran rina a kaba: Gwamnatin Kaduna ta gindaya sharuda 7 masu tsauri a kan fitar Zakzaky kasar Indiya

Dan sandan ya cigaba da fada wa kotun cewa, "maimakon lauya Ali ya gabatar da wanda ya ke kare wa, sai ya taimaka masa ya gudu, lamarin da ya kawo cikas a binciken da 'yan sanda ke gudanar wa a kansa."

Sai dai, bayan an gama karanta wa lauyan laifukan da ake zarginsa da aikata wa, sai ya ce sam bai aikata hakan ba.

Alkalin kotun, Ibrahim Kagarko, ya amince da bawa lauyan belin kansa da kansa tare da daga cigaba da sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel