Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari

Matakan da zan dauka kan rikicin Majalisun Bauchi da Edo - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai yi aiki da hukumomin da suka dace domin warware rikicin da ke faruwa a Majalisar Jihar Edo da Jihar Bauchi.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin wata tawagar mambobin Majalisar Jihar Bauchi da wasu masu ruwa da tsaki a jihar.

Shugaba Buhari ya ce, "Na san da matsalar da ake fama da ita a Majlisun Jihohin Edo da Bauchi kuma ina la'akari da matsayi na a matsayin shugaban kasa da yanayin siyasar kasar da kuma kundin tsarin mulkin kasa da ayyukan kwamishinonin 'yan sanda da jam'iyyun siyasa. A kowanne lokacin ina son in rika biyaya ga abinda kundin tsarin mulki ya tanada."

DUBA WANNAN: Wata mata tayi yunkurin siyan mota da kudin jabu da ta buga a gidanta

Ya yi alkawarin cewa zai yi aiki tare da Mnistan Shari'a bayan an rantsar da shi da kuma Sufeta Janar na 'Yan sanda domin tabbatar da cewa ba a tauye hakokin mazabu ko al'umma ba.

Shugaban kasar ya bukaci mambobin jam'iyyar su cigaba da kare hakokin su da na wadanda suka zaba tare da tabbatar da cewa kawunnan 'yan jam'iyyar bai rabu ba.

Ya shawarce su da cigaba da gudanar da ayyukan su bisa tsarin doka tare da cigaba da fadakar da 'yan jam'iyyar a matakin jiha da kasa.

Mambobin jam'iyyar ta APC karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole sun yi wa shugaban kasa jawabi kan abubuwan da suka haifar da rikicin a Majalisar ta Jihar Edo.

Majalisar na Jihar Bauchi ta rabu kashi biyu, bangare daya na biyaya ga gwamnan Bala Muhammad na jam'iyyar PDP. Dayan bangaren kuma ana tsamanin ya kunshi mafi yawancin 'yan majalisar jam'iyyar APC ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel