Rundunar soji tayi martani kan bindige 'Yan sanda 3 da dakarunta su kayi a Taraba

Rundunar soji tayi martani kan bindige 'Yan sanda 3 da dakarunta su kayi a Taraba

Rundunar Sojojin Najeriya ta ce an janyo hankalin ta kan wata sanarwa da Kakakin Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Frank Mba ya fitar mai lamba CZ.5300/FPRD/FHQ/ABJ/VOL.2/68 a ranar 7 ga watan Augustan 2019 kan mummunan lamarin da ya faru a ranar 6 ga watan Augustan 2019 inda sojojin bataliya ta 93 da ke Takum su kayi musayar wuta da suke zargin masu garkuwa da mutane ne amma daga bisani aka gano 'Yan sandan binciken sirri ne daga hedkwatan 'Yan sanda daga Abuja wadda hakan ya yi sanadiyar rasuwar wasu sannan wasu suka jikkata.

Sanarwar ta ce,"A ranar 6 ga watan Augustan 2019, Dakarun Sojojin Najeriya sun yi musayar wuta da wasu da suke tsamanin masu garkuwa da mutane ne da suka sace wani mutum a titin Ibi - Wukari a jihar Taraba.

"Wadanda akayi zargin masu garkuwa da mutanen kimanin su 10 suna cikin farar bas ne mai lamba LAGOS MUS 564 EU sun ki tsayawa ne duk da cewa sojojin sunyi yunkurin tsayar da su har sau uku. Rashin tsayawar ya sanya sojojin suka bi motar kuma wadanda ke motar suka fara harbi hakan ya sa sojojin suma suka bude musu wuta.

DUBA WANNAN: Cin amana: Nayi nadamar kyalle mata ta shiga siyasa - Wani magidanci ya fada wa kotu

"Yayin musayar wutan mutane hudu sun mutu nan take yayin da wasu hudu suka samu rauni kuma mutum biyu ba a gano inda suke ba. Bayan musayar wutan ne daya daga cikin wanda ya samu raunin ya bayyana cewa su jami'an 'Yan sandan sirri ne daga hedkwatan 'Yan sanda na Abuja da aka aiko su kamo wani.

"Kwamandan sojojin ya tambayi wani jami'in dan sanda ko ya san cewa wata tawagar 'Yan sanda daga Abuja ta zo yin aiki a garin amma ya ce Hedkwatan 'Yan sanda ba ta sanar da su ba wadda hakan ya kara tabbatar da abinda mazauna garin suka fadawa sojojin cewa masu garkuwa da mutane ne suka sace wani.

"Hadin gwiwa da sadarwa tsakanin 'Yan sanda da sojojin shine hanyar kiyaye afkuwar irin wannan lamarin duba da cewa dukkansu suna yaki ne da bata gari musamman a wannan lokacin da ake fama da kallubalen tsaro a kasar.

"Domin kare afkuwar irin wannan a gaba, Hedkwatan 'Yan sanda da Hedkwatan Rundunar Sojojin Najeriya sun kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa karkashin jagorancin mataimakin sufeta Janar na 'Yan sanda mai kula da sashin masu binciken manyan laifuka, DIG Mike Ogbizi domin gano gaskiyar abinda ya faru.

"Saboda haka ba dai-dai bane a fitar da bayani a hukumance kan abinda ya faru har zuwa lokacin da kwamitin ya ta kammala binciken ta kan abinda bai kamata ya faru ba tun farko."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel