Da sauran rina a kaba: Gwamnatin Kaduna ta gindaya sharuda 7 masu tsanani a kan fitar Zakzaky kasar Indiya

Da sauran rina a kaba: Gwamnatin Kaduna ta gindaya sharuda 7 masu tsanani a kan fitar Zakzaky kasar Indiya

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar neman wata babbar kotu da ke jihar da ta bata izinin kakaba wasu sharuda guda 7 ga shugaban mabiya Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wanda zai fita kasar Indiya tare da matarsa, Zeenat, domin a duba lafiyarsu.

A ranar litinin wata babbar kotun jihar Kaduna ta amince da bayar da belin Zakzaky domin ya fita zuwa kasar Indiya a duba lafiyarsa, kamar yadda lauyoyinsa suka buta.

A takardar sabuwar karar da ta shigar, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana girmama 'yancin duk wani mutum na sa.

Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar neman wata babbar kotu da ke jihar da ta bata izinin kakaba wasu sharuda guda 7 ga shugaban mabiya Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wanda zai fita kasar Indiya tare da matarsa, Zeenat, domin a duba lafiyarsu.

A ranar litinin wata babbar kotun jihar Kaduna ta amince da bayar da belin Zakzaky domin ya fita zuwa kasar Indiya a duba lafiyarsa, kamar yadda lauyoyinsa suka buta.

A takardar sabuwar karar da ta shigar, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana girmama 'yancin duk wani mutum na neman lafiya, amma tana son kotun ta tabbatar musu da wasu sharuda guda 7 da suke son a cika kafin su amince da fitar Zakzaky zuwa kasar Indiya neman lafiya.

1. Muna son ma'aikatar kasar waje ta nada wakilan da zasu kulla duk wasu tsare-tsare tsakanin Zakzaky da asibitin 'Medanta' da ke kasar Indiya tare da gudanar da duk wani shiri da ake bukatar kulla wa tsakanin kasa da kasa idan da bukatar gwamnati ta kai wani mutum don a duba shi a kasar ketare.

2. Duk da za a yi tafiyar ne tare da wakilan gwamnati, kowanne bangare shine zai biya wa 'yan tawagarsa kudin zuwa da na dawowa da na binci da muhallin kwana da sauran walwala. Kuma sai kowanne bangare ya saka hannu a kan rantsuwar cewa da zarar an sallame shi daga asibiti, za a dawo Najeriya domin cigaba da Shari'a.

DUBA WANNAN: Abu 5 da ya kamata ku sani a kan asibitin da za a kai Zakzaky a kasar Indiya

3. Dole kowanne bangare ya kawowa kotu shaidunsa guda biyu, daya a cikinsu dole ya kasance babban sarki mai daraja ta daya. Dole dukkan shaidun su kasance masu kadara babba a cikin birnin Kaduna, sannan kuma su saka hannu zasu gabatar da wadanda suka tsaya wa a gaban kotu, duk lokacin da ake bukatar hakan.

4. Ba zamu yarda ya fita ba sai gwamnatin tarayya ta samu tabbas daga gwamnatin kasar Indiya a kan ba zata saurari duk wata murya da zata nemi a bawa Zakzaky da matarsa mafaka ba a kasar ko shi Zakzaky da matarsa su yi amfani da wata siga ko salo na ganin ya cigaba da zama a asibiti ko cikin kasar da sunan dan gudun hijira ko fursunan siyasa ba.

5. Dole kowanne bangare su rubuta yarjejeniya da lauyoyinsu zasu sa hannu, a kan cewa babu wanda zai yi wani yunkuri na kawo cikas a shari'ar da ake yi yayin da wadanda ake kara suke asibiti don neman lafiya a asibitin kasar Indiya..

6. Sai gwamnatin tarayya ta samar da jami'an tsaro da zasu raka tawagar masu tafiya daga kowanne bangare, kuma su saka ido a kansu tare da sako su a gaba a dawo Najeriya da zarar an sallame su daga asibiti.

7. Babu wani mutum da zai ziyarci Zakzaky da matarsa a kasar Indiya ba tare da ya bi ta hannun ofishin jakadancin Najeriya ba domin a tantance shi da tabbatar da manufarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel