Buhari ya rattaba hannu a kan wasu sabbin dokoki guda hudu

Buhari ya rattaba hannu a kan wasu sabbin dokoki guda hudu

A ranar Laraba, 07 ga watan Agusta, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu a kan wasu sabbin dokoki guda uku da majalisar da ta gabata ta zartar da su.

Sabbin dokokin guda uku su ne; na kafa hukumar kula da kadarorin gwamnati (Asset Management Corporation of Nigeria) wanda aka yi wa garambawul a shekarar 2019, hukumar asusun kudin fanshon jami'an tsaro (Defence Intelligence Agency Civilian Pensions Board) wacce aka yi wa garambawul a shekarar 2019 da kuma na kafa hukumar 'National Biosafety Management Agency.

Ita Enang, mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren harkokin da suka shafi majalisar dattijai, ne ya sanar da hakan a cikin wani sako da ya aike wa manyan kafafen yada labarai na kasa.

A cewar sanarwar, aikin hukumar 'Asset Management Corporation of Nigeria (AMCON)' zai hada da kwato dukiyar kasa daga hannun jama'a ko masana'antun da ake bi bashi tare da saka ido a kan asusunsu na ajiya da ke dukkan bankunan kasar nan.

DUBA WANNAN: Wani karamin yaro dan Boko Haram ya gwada yadda aka koya masa harbi da sarrafa bindiga (Hotuna)

Ita kuma hukumar 'Defence Intelligence Agency Civilian Pensions Board' za ta ke kula da batun fansho na farar hula da ke aiki a hukumomin tsaro bayan sun bar aiki ko mutuwa yayin aiki.

'National Biosafety Management Agency' za ta kula da tabbatar da tsaron lafiya da muhalli daga dukkan wata barazana da kan iya taso wa sakamakon amfani da sinadarai da makamashi masu kwayoyin zarra na halittu (Bio-Security)

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel