Eid-el-Kabir: Obaseki ya bada umarnin biyan albashin watan Agusta kai tsaye

Eid-el-Kabir: Obaseki ya bada umarnin biyan albashin watan Agusta kai tsaye

-Gwamnan jihar Edo zai biya ma'aikatan jihar albashin Agusta tun kafin watan ya kai karshe saboda su yi bikin sallah cikin wadata

-Mai ba gwamnan shawara kan lamuran yada labarai, Crusoe Osagie ne ya bada wannan sanarwa ranar Laraba a babban birnin jihar Edo

-Crusoe ya ce burin gwamnatinsu a kullum shi ne faranta ran ma'aikatanta

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki ya bada umarnin biyan ma’aikatan jiharsa albashinsu na watan Agusta domin su gudanar da bikin sallah babba cikin farin ciki.

Gwamnan ya bada wannan umarnin ne a wurin ganawar mako-mako ta majalisar zartarwar jihar Edo ranar Laraba a fadar gwamnatin jihar dake Benin City.

KU KARANTA:Matawalle ya sallami dukkanin sakatarorin kananan hukumomin Zamfara 14 daga aiki

Dama can ma’aikatan gwamnati a jihar Edo sun saba karbar albashinsu ne a ranar 26 ga ko wane wata bisa burin gwamnatin jihar na faranta ran ma’aikatanta.

A wani zancen da ya fito daga hannun mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Crusoe Osagie ya ce gwamnan na so ne ma’aikatan su yi bikin sallah da isassun kudi a hannunsu.

A cewarsa: “ Gwamnatin jiha na sane kwarai da gaske da bukatun ma’aikatanta musamman mabiya addinin musulunci a irin wannan lokaci na bikin sallah. A dalilin hakan ne ya sanya gwamnan ya fito da wannan salo na biyan ma’aikatan kafin watan Agusta ya kai karshe.”

Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar za ta cigaba da jajircewa domin ganin ta faranta ran ma’aikatan ta yadda za su dada dagewa wurin kawo cigaba mai inganci a jihar ta Edo.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa, zaku ji cewa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya sauya sakatarorin kananan hukumomin Zamfara su 14.

Har ila yau, gwamnan ya nada sabbin shugabanin kwalejin kimiyya da kere-kere ta Abdu Gusau wadda ke Talata Mafara da kuma na kwalejin ilimi ta jihar Zamfara wadda aka fi sa ni da COE, Maru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel