Yanzu-yanzu: Sojoji sun kashe 'Yan sanda uku a Taraba, sun saki wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da aka kamo

Yanzu-yanzu: Sojoji sun kashe 'Yan sanda uku a Taraba, sun saki wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane da aka kamo

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta sanar da kashe jami'an uku da kuma raunata wasu da dama yayin da dakarun sojojin Najeriya suka bude wa tawagar 'yan sanda wuta a Taraba.

Lamarin ya faru ne a titin Ibi zuwa Jalingo a cewar 'Yan sanda.

Felix Adojie, mataimakin sufritandan 'yan sanda ya jagoranci tawagar 'yan sandan ne domin kamo wani mutum da ake zargin shugaban masu garkuwa da mutane ne da aka ce sunan sa, Alhaji Hamisu.

DUBA WANNAN: 2019: APC za ta iya lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa - Goodluck Jonathan

Sojojin sun kaiwa 'yan sandan hari ne ta hanyar bude musu wuta a cewar mai magana da yawun 'yan sanda Frank Mba.

'Yan sandan suna hanyarsu na kai Mr Hamisu zuwa Hedkwatan 'Yan sanda da ke Jalingo ne yayin da sojojin suka bude musu wuta duk da cewa akwai hujjar cewa su 'yan sanda ne da ke bakin aikinsu kamar yadda doka ta basu dama.

An ruwaito cewa sun kashe sufetan 'yan sanda daya da wasu masu mukamin saja biyu tare da raunatta wasu. Sun kuma kashe farar hula guda daya.

"Sojojin sun kuma saki wadanda ake zargin wata Alhaji Hamisu wanda yanzu ba san inda ya ke ba," inji 'Yan sandan.

'Yan sandan sun ce Mr Hamisu rikaken shugaban masu garkuwa da mutane ne da aka dade ana nema ruwa a jallo da ake zargi da hannu cikin satar mutane a Taraba ciki har da sace wani dilalin man fetur a garin a baya-bayannan.

Dilalin man da ba a bayyana sunansa ba ya biya kudin fansa naira miliyan 1 kafin aka sako shi inji 'Yan sandan.

"Sufeta Janar na 'Yan sanda, Muhammad Adamu ya bayar da umurnin gudanar da sahihin bincike kan afkuwar mummunan lamarin, a cewar mataimakin kwamishinan 'yan sanda Mr Mba.

An yi yunkurin ji ta bakin mai magana da yawun sojoji, Sagir Musa amma bai amsa wayarsa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel