'Na gaji da fyade da miji ne ke yi min', inji wata mata da ke neman kotu ta raba aurenta

'Na gaji da fyade da miji ne ke yi min', inji wata mata da ke neman kotu ta raba aurenta

Wata 'yar kasuwa mai suna Charity John, a ranar Laraba ta roki wata kotu da ke zamanta a Jikwoyi Abuja ta raba aurenta da mijinta Abel saboda ikirarin da ta yi na cewa yana yi mata 'fyade'.

A cikin karar da ta shigar na neman kotu ta raba aurensu, Charity ta ce: "Miji na yana son yi min fyade. Na jure hakan na lokaci mai tsawo."

Ta kuma yi ikirarin cewa mijinta yana biye-biyen 'yan mata a waje.

A yayin da ya ke mayar da magana a kotun, Abel, dan kasuwa ya musanta dukkan zargin da matarsa tayi masa.

DUBA WANNAN: 2019: APC za ta iya lallasa PDP a zaben gwamnan Bayelsa - Goodluck Jonathan

"Duk karya ta fadi. Ba zan iya yi wa mata ta fyade ba. Kuma bana neman mata, hasali ma mata ta ce ke bin 'yan maza a waje.

"A watan Mayun 2017 lokacin tana wanka a ban daki. Na ga sakon kar ta kwana da wani mutum a China ya aiko mata. Suna tattaunawa da mutumin.

"Sun shirya cewa za suyi aure. Ta fada masa cewa ba ta da aure kuma da dan uwanta ta ke zama ba mijin ta.

"Da ta tunkare ta da batun sai ta kwace wayar daga hannu na ta fasa a kasa. Na gaji da wannan auren," a cewar mijin ta.

Abel ya amince alkali ya raba auren kuma ya ce zai rike yaran su biyu da suka haifa tunda matar ta nuna ba ta son yaran.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta ruwaito cewa Alkalin kotun, Jamilu Jega ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Augusta domin yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel