Wani karamin yaro dan Boko Haram ya gwada yadda aka koya masa harbi da sarrafa bindiga (Hotuna)

Wani karamin yaro dan Boko Haram ya gwada yadda aka koya masa harbi da sarrafa bindiga (Hotuna)

Wani karamin yaro dan kungiyar Boko Haram da aka kama ya gwada yadda aka basu horon harbi da bindiga da kuma sarrafa makami yayin yaki.

Yaron, wanda bai wuce shekaru 15 ba a duniya, ya gwada yadda ake rike bindiga da saka harsashi da kuma harba ta. Kazalika, ya nuna irin yadda ya kamata mutum ya tsaya ko tsuguna wa yayin da yake rike da bindiga.

Kungiyar Boko Haram na amfani da kananan yara maza da mata wajen kai hare-hare a jihar Borno, musamman wajen kai harin kunar bakin wake.

Wani karamin yaro dan Boko Haram ya gwada yadda aka koya masa harbi da sarrafa bindiga (Hotuna)
Wani karamin yaro dan Boko Haram ya gwada yadda aka koya masa harbi da sarrafa bindiga
Source: Instagram

Ko a yau (Laraba), sai da wasu kananan yaran mata guda biyu yan kunar bakin wake suka tayar da bama bamai a jahar Borno, inda suka kashe mutane guda uku, sa’annan suka raunata wasu mutane Takwas, inji rahoton jaridar Guardian.

DUBA WANNAN: Toh fa: Mijina na kwanciya da mata masu tabin hankali - Matar aure ta fada wa kotu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Borno, SEMA, Bello Danbatta ya bayyana cewa yan kunar bakin sun kai harin ne da yammacin Talata da misalin karfe 8:30 na dare a yankin Mafa.

Boko Haram sun shafe kusan shekara 10 kenan suna yaki da gwamnatin Najeriya da nufin kafa daular Musulunci a Najeriya, kuma suna amfani da kananan yara musamman mata wajen kai harin kunar bakin wake a masallatai, kasuwanni, gidajen kallo, teburin mai shayi, da kuma tashoshin mota.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel