Sowore bai da ikon da zai kira zanga-zangar juyin juya hali - Oshiomhole

Sowore bai da ikon da zai kira zanga-zangar juyin juya hali - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa kowani dan Najeriya na da daman gudanar da zanga zanga amman dole sai sun fahimci tsarin da ya dace su bi don gabatar da korafe-korafen su.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawar da kwamitin APC na kasa tayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, Abuja.

Don haka yayi Allah wadai da zanga-zangar juyin juya hali da jagoran kungiyar Global Coalition for Security and Democracy, Omoyele Sowore ya shirya.

A cewar shi, Sowore wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar African Action Congress (AAC) kuma mai wallafa labarai a shafin Sahara Reporters, ya yanke shawarar jagorantar zanga zangar ne bayan ya fadi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Jam'iyyar SDP ta kori Farfesa Jerry Gana, ta fadi dalili

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Adams Oshiomhole a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, ya sha alwashin cewa jam’iyyar ba za ta kunyata yan Najeriya ba.

Oshiomhole ya fadi haka ne a wani ganawa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kawmitin jam'iyyar na kasa a fadar shugaban kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel