Atiku ne 'ummul aba'isin' fatara da talaucin da ake fama da shi a Najeriya - BMC

Atiku ne 'ummul aba'isin' fatara da talaucin da ake fama da shi a Najeriya - BMC

Kungiyar magoya bayan Buhari ta 'Buhari Media Organisation' ta zargi tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugbana kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a matsayin wanda ya janyo yawan talaucin da ake fama da shi a kasar.

BMO ta ce PDP ce ta jefa 'yan Najeriya cikin talauci yayin da ta ke mayar da martani kan wata jawabi da aka ce Atiku Abubakar ya yi na sukar gwamnatin Buhari na laifin talauta 'yan Najeriya kamar yadda rahoton UNDP ta nuna.

A jawabin da su kayi a ranar Talata, Shugaban BMO, Niyi Akinsiju da Sakataren kungiyar Cassidy Madueke sun ce a karkashin gwamnatin PDP ne aka samu karin adadin mutanen da ke rayuwa da kasa da dalla 1.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

Ya ce hukumar ta UN ta ce kimanin 98 cikin 100 na 'yan Najeriya ne ke fama da matsananincin talauci amma dan takarar shugaban kasar na PDP bai fahimci rahoton ba kafin ya fara sukar shugaban kasar.

"Rahoton ya nuna cewa a halin yanzu 'yan Najeriya 46 cikin 100 ne ke rayuwa cikin talauci amma idan Atiku bai manta ba 60.9 cikin 100 na 'yan Najeriya ne ke rayuwa cikin talauci a shekarun 2010 da 2012 a cewar Bankin Duniya, wacce ita ce hukumar da ke kididigan talauci a duniya." inji shi.

Ya ce a wannan lokacin ne Atiku ke ganiyar satar kadarorin Najeriya wadda hakan ya sanya shi rikici da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

"Ya sayar da kadarorin gwamnati a farashin mai rahusa ga abokansa kuma hakan ya sanya ma'aikata da dama suka rasa ayyukansu ba tare da an biya su hakokinsu ba kuma a lokacin ne ya sayar wa kansa daya daga cikin kadarorin wata 'Onne Port."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel