Cin amana: Nayi nadamar kyale mata ta shiga siyasa - Wani magidanci ya fada wa kotu

Cin amana: Nayi nadamar kyale mata ta shiga siyasa - Wani magidanci ya fada wa kotu

Wani dilalin man fetur mai yara biyar, Mr Wasiu Badmus, a ranar Laraba ya shaidawa kotu cewa ya yi nadamar kyale matarsa, Suliyat shiga siyasa saboda a cewarsa a yanzu da zama karuwa.

Badmus ya fadi hakan ne yayin da ya ke kare kansa daga zargin barazanar kashe matarsa a gaban Chief Ademola Odunade, Shugaban Kotun Mapo da ke Ibadan inda ya ce tun da ya kyale matarsa ta shiga jam'iyyar siyasa ta fara bijire masa.

Badmus ya ce ya gargadi Suliyat cewa maza sun fiye neman mata da suka shiga siyasa a lokacin da ta fada masa tana son shiga siyasa amma ya yarda saboda a lokacin ya amince da ita.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

"Tun da Suliyat ta fara zuwa gangamin yakin neman zabe da taron siyasa na fara jin labarai marasa dadi game da ita kan yadda ta ke bin mazaje.

"Hasali ma, a ranar 28 ga watan Fabrairu na ga wani babban dan siyasa a garin mu ya dawo da ita gida misalin karfe 11.30 na dare kuma ban ji dadin hakan ba.

"Tun daga wannan lokacin ba ta dawo wa gida sai bayan 12 na dare kuma ta dena bin umurni na.

"Bayan wasu kwanaki kuma, 'yan banga sun fada min cewa wani babban dan siyasa a unguwar mu ya sake dawo da ita gida cikin dare kuma nima na gansu tare.

"Bugu da kari na ji Suliyat a wayar tarho tana shirya inda za su hadu da wani mutum," a cewar Badmus.

A baya, Suliyat ta fadawa kotu tana son a raba auren domin mijinta yana sa ido kan inda ta ke zuwa kuma yana barazanar kashe ta.

"Badmus yana cin zali na har ta gai ka bana samun kwanciyar hankali tare da shi," a cewar Suliyat.

Alkalin kotun ya raba auren kuma ya bawa Badmus damar rike yaransu biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel