Da duminsa: Jam'iyyar SDP ta kori Farfesa Jerry Gana, ta fadi dalili

Da duminsa: Jam'iyyar SDP ta kori Farfesa Jerry Gana, ta fadi dalili

- Jami'iyyar Social Democratic Party, SDP, ta kori Farfesa Jerry Gana daga jam'iyyar

- Jam'iyyar ta kore shi ne bisa ikirarin cewa ya zame mata alakakai

- An cimma matsayar korarsa daga jam'iyyar ne sakamakon shawarwarin da shugabanin jam'iyyar na jihar Niger suka bayar

Jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, ta kori tsohon dan takarar shugaban kasar ta, Farfesa Jerry Gana bayan ta zarge shi da zama matsala ga jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar na yankin Arewa Ta Tsakiya, Abubakar Dogara ne ya bayar da sanarwar a ranar Laraba, 7 ga watan Augusta a garin Jos na jihar Plateau.

A cewar sanarwar, jam'iyyar ta kuma kori Alfa Muhammed daga kwamitin amintattu na jam'iyyar kamar yada Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: PDP ta dakatar da shugabaninta 5 da wasu mutane 9 a Kebbi

Sanarwar ta ce an cimma matsayar korar mutane biyun ne bayan wani taro da shugabanin jam'iyyar na jihar Niger karkashin jagorancin Bukhari Yakubu-Yarima suka bayar.

"Shugabanin jam'iyyar SDP reshen jihar Niger karkashin jagorancin Barr. Bukhari Yakubu Yarima sun sake jadadda korar Farfesa Jerry Gana da Alfa Muhammed daga jam'iyyar SDP da Kwamitin amintattu na kasa tayi.

"Farfesa Gana bai taba kawo wata amfani a jam'iyyar ba a jihar Niger sai dai yadda kiyaya da rikici tsakanin 'yan jam'iyya," inji sanarwar.

Idan ba a manta ba da a watan Fabrairu, kwamitin masu zartarwa na jam'iyyar ta SDP sun bayar da shawarar korar Farfesa Gana daga jam'iyyar saboda saba wasu dokoki da yi wa jam'iyya zagon kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel