APC ba za ta yi bacci ba har sai ta cika alkawaran da ta dauka – Oshiomhole

APC ba za ta yi bacci ba har sai ta cika alkawaran da ta dauka – Oshiomhole

- Adams Oshiomhole, Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yace jam’iyyarsa za ta cika alkawaran da ta daukar ma yan Najeriya

- Oshiomhole ya bayyana APC a matsayin jam’iyyar talakawan Najeriya, kuma ta mayar da hankali ga sake gina talakawa

- Shugaban jam’iyyar na APC ya bayyana cewa ita ke da ragamar gwamnatin kasar

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, ya sha alwashin cewa jam’iyyar ba za ta kunyata yan Najeriya ba.

Oshiomhole ya fadi haka ne a wani ganawa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kawmitin jam'iyyar na kasa a fadar shugaban kasa.

Wani mai sharhi a kafofin yada labarai kuma hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, ya kawo inda Oshiomhole ke cewa APC na shirin kafa cibiyar karatun harkokin ci gaba don aiwatar da manufar jam’iyyar.

Yace shugaban jam’iyyar na kasa har ila yau ya bayyana APC a mastayin jam’iyyar talakawan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yadda nayi rayuwa tsawon shekara 2 tare da yan ta’addan Boko Haram – Wani bawan Allah

Legit.ng ta rahoto a baya cewa Oshiomhole da kwamitin jam’iyyar za su gana da shugaban kasa Buhari a fadar shugaban Kasar.

A cewar The Nation, ganawar zai tattauna batutuwan da suka shafi zaben 2019 na kasa da kuma samar da matakan da za su tabbatar da matsayin jam’iyyar don ci gaban kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel