Gwamnatin jihar Katsina ta haramta sayar da baburan 'yan Boko Haram

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta sayar da baburan 'yan Boko Haram

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta sayar da babur mai kafa biyu kirar 'Boxer' da aka fi kira da 'Boko Haram' a fadin jihar, tare da bayyana yin hakan a matsayin daya daga cikin matakan dakile aiyukan ta'addanci da suka addabi sassan jihar a 'yan kwanakin baya bayan nan.

Da yake sanar da sabuwar dokar a ranar Laraba, kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) reshen jihar Katsina, Ali Tanimu, ya ce majalisar tsaro a jihar Katsina ta bayar da umarnin fara kamen 'yan acaba da direbobin adadaita sahu marasa rijista.

Tanimu ya bayyana cewa an haramta sayar da babur din 'Boko Haram' ne saboda juriya da karfin da babur din keda shi, musamman wajen bin hanyoyin jeji masu rairayi ko tsaunuka, lamarin da yasa 'yan ta'adda koda yaushe ke amfani da shi wajen kai hari.

Kwamandan na wadannan kalamai ne yayin da ya jagoranci jami'an FRSC a wata ziyara da suka kai zuwa ofishin kungiyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta.

DUBA WANNAN: Babbar magana: An kama wasu mutane biyu dake basaja a matsayin Buhari da Osinbajo

A cewarsa, "an bayar da umarnin fara kamen 'yan acaba da masu adaidaita da basu da rijista, saboda suna amfani da rashin rijistar wajen aikata laifuka. Babu bayanansu a ko ina, hakan ya sa gano su yake yin wuya duk lokacin da suka aikata wani laifi.

"Muna fuskantar matsala da direbobin adaidaita sahu da ke amfani da labule masu launi daban-daban wajen rufe kofofin baburansu, hakan yana hana a gane fasinjojin da suka debo, lamarin da ya zama barazana ga harkar tsaro.

"Mun samu umarni daga majalisar tsaro domin fara kamen 'yan acaba da adaidaita da basu da rijista daga karshen watan nan, a saboda haka ne muke bukatar hadin kan 'yan jarida domin su taimake mu wajen wannan aiki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel