Wata budurwa 'yar Najeriya ta ajiye aikin da ake biyanta naira miliyan 22, saboda tana so ta bude nata kasuwancin

Wata budurwa 'yar Najeriya ta ajiye aikin da ake biyanta naira miliyan 22, saboda tana so ta bude nata kasuwancin

- Wata budurwa ta bayyana wani cigaba da ta samu a rayuwarta

- Inda ta bayyana cewa ta ajiye aikin da take yi wanda ake biyanta kudi sama da naira miliyan ashirin da biyu domin ta fara yin kasuwancin ta

- Budurwar ta bayyana cewa yanzu haka ta siyi sabon gida ta kuma samu sabon ofishintaa wanda za ta yi kasuwancinta a ciki

Wata budurwar 'yar Najeriya mai shekaru 25 ta bayyana wani wani cigaba da ta samu a rayuwarta, yayin da ta siyi sabon gida sabuwar mota, sannan ta shiga sabon ofishinta bayan ta ajiye aikin da ake biyanta naira miliyan ashirin da biyu.

Budurwar mai suna Lola ta wallafa labarin nata a shafin sada zumunta na Twitter, ta rubuta cewa:

"Allah na gode ma, kuma kai ne abin godiya a koda yaushe, mako biyu kawai da suka wuce na ajiye aikina wanda ake biyana naira miliyan ashirin da biyu.

KU KARANTA: Wani Bafaranshe ya kera injin tashi sama mai tsananin gudu

"Yanzu na dawo sabon ofishina domin na fara kasuwancin da na jima ina mafarki yi, kuma na siyi sabon gida, duka kuma shekaruna ashirin da biyar a duniya."

Wannan lamari na budurwar ya faru a kasar waje ne, yayin da a kasa Najeriya mutane ke fama da albashin naira dubu sha takwas kacal a wata, banda rashin aikin yi da yayi katutu a lungu da sako na kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel