Tashin bama-bamai ya kashe mutum 14 a Kabul

Tashin bama-bamai ya kashe mutum 14 a Kabul

-Wani harin bam ya kashe mutum 14 a Kabul babban birnin kasar Afghanistan

-Kungiyar Taliban ta yi ikirarin cewa ita ta kai harin duk da cigaba da ake na tattaunawa tsakaninta da kasar Amurka domin yin sulhu

-Masana masu sharhi sun ce akwai alamun haske a zaman da akayi a kasar Qatar a karshen mako

Akalla mutum 14 ne suka mutu sannan kimanin 150 sun samu munanan raunuka a sakamakon tashin wani bam da dauke a cikin wata mota wadda ta nufi ofishin ‘yan sandan Kabul, babban birnin Afghanistan.

Kungiyar Taliban tayi ikirarin kai wannan harin wanda ke zuwa a daidai lokacin da ake tsakiyar tattaunawa tsakanin Amurka da ‘yan kungiyar.

KU KARANTA:Eid-el-Kabir: Hukumar tsaro ta NSCDC za ta baza jami’ai 4,000 a Abuja lokacin bikin babbar sallah

Dukkanin bangarorin guda biyu sun ce ana samun cigaba a tattaunawar da akeyi wadda ke kokarin kawo karshen rikicin da ya kwashi tsawon shekaru 18 ana yinsa.

Har ila yau, kungiyar Taliban ta ce, ita ke da alhakin wannan harin bam da aka kai, inda take cewa cibiyar daukar jami’an tsaro ta nufa da harin kuma tayi nasarar kashe ‘yan sanda da sojoji da dama.

Da alamar har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da warware rikicin da ya dade yana damun kasar Afghanistan ya ki ci ya ki cinyewa.

Sai dai kuma masana dake sharhi kan wannan al’amari na ganin akwai haske dangane da wannan lamari, a sakamakon zaman tattaunawa da ya wakana tsakanin Amurka da Taliban a karshen mako.

Wakilin Amurka na musamman, Zalmay Khalilzad ya fadi cewa an samu cigaba sosai a yayin zaman tattaunawan da akayi a Qatar a karshen mako, kuma yana fatan tattaunawar za ta cigaba nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel