Kwastam sun kama buhuna 1, 940 na shinkafar kasar waje a Neja

Kwastam sun kama buhuna 1, 940 na shinkafar kasar waje a Neja

Ma’aikatan da ke yaki da fasa-kauri na reshen jihar Neja sun yi ram da wasu motoci dauke da buhunan shinkafa na kasar waje da a ke zargin cewa an shigo da su ne ta barauniyar hanya.

Kamar yadda mu ka samu labari, Jami’an hukumar kwastam sun tare wannan mota ne cike da buhuna 1, 940 na shinkafar waje da a ka yi fasa kaurin su wanda kudin su ya haura miliyoyi.

Shugaban jami’an Kwastam na yankin Neja, Abba-Kassin Yusuf ne ya bayyanawa Manema labarai wannan cikin babban birnin Neja na Minna a Ranar Laraba, 7 ga Watan Agusta, 2019.

Babban Jami’in ya ce Ma’aikatan na sa sun kama wadannan motoci ne a wurare daban-daban. A Garin Mokwa an tare wata mota dauke da buhunan shinkafa 520 da kuma buhunan sukari a boye.

KU KARANTA: EFCC: Shugaban Manoma ya saci Maganin feshi da takin zamani a Zamfara

Wadanda a ka kama sun boye buhunan sukari 50 ne a cikin shinkafar da a ka riga a ka biya kudin shigowarsu. Kudin buhunan wannan sukari da a ka karbe ya kai N697, 000 inji Jami’in.

Abba-Kassin Yusuf ya kara da cewa a kan titin Minna-Lambata-Suleja, sun yi nasarar kama wasu buhuna 700 na shinkafa. Kudin shigo da wannan kaya ya kusa Naira miliyan 12 inji Jami’in.

Kassin Yusuf ya yi wannan hira da Manema labarai ne ta bakin DCP Jalo Ibrahim. Hukumar ta kuma kama wata mota dauke da shinkafa da a ka shirya kamar kayan siminti na Miliyan 12.4.

A cewar jami’in na Kwastam, yanzu sun kudiri niyyar maganin masu shigo da kaya ta barayin hanyoyi. Kassin Yusuf ya ce aikinsu ya na kyau kuma za su fara bin kan iyakokin jihar Kogi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel