Eid-el-Kabir: Hukumar tsaro ta NSCDC za ta baza jami’ai 4,000 a Abuja lokacin bikin babbar sallah

Eid-el-Kabir: Hukumar tsaro ta NSCDC za ta baza jami’ai 4,000 a Abuja lokacin bikin babbar sallah

-Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC za ta baza jami'ai dubu hudu a birnin Abuja lokacin bikin sallah babba

-Kwamandan hukumar na Abuja, Patrick Ukpan ne ya bada wannan sanarwar ta hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar ranar Talata a Abuja

-A cewar kwamandan labari ne ya zo masu cewa akwai masu shirin tayar da zaune tsaye lokacin bikin sallar don haka dole su dauki mataki

Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC ta ce za ta baza jami’ai 4,000 domin su kula da tsaron babban birnin tarayya Abuja lokacin bikin sallah babba.

Kwamandan hukumar na Abuja, Patrick Ukpan shi ne ya bayar da sanarwar ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Akinbinu David ranar Talata, inda ya ce za a zakulo jami’an ne daga dukkanin sassan hukumar tasu dake Abuja.

KU KARANTA:Matawalle ya sallami dukkanin sakatarorin kananan hukumomin Zamfara 14 daga aiki

A cikin sanarwar, ya fadi cewa za a samu kwararrun jami’ai daga fanni daban-daban na hukumar ta NSCDC, domin tabbatar da an samar da tsaro yadda ya kamata.

Ukpan ya ce: “ Zamu tura da jami’anmu ko wane lungu da sako dake Abuja, zamu tabbatar mun tsare ko ina da ko ina a lokacin da ake bikin babbar sallah.

“ Akwai wuraren da zamu bai wa kulawa ta musamman kamar irin kasuwanni, tashoshin mota, filin sallar idi, wurin wasan yara da kuma kan iyaka saboda wurare ne wadanda suke da tarin jama’a a lokutan irin wadannan. Zamu samar da tawagar sinitiri ta awa 24 a wadannan wuraren.” A cewar Ukpan.

Haka zalika, hukumar ta bayyana mana cewa, ta samu labarin akwai wasu gungun bata gari da ke da niyyar tayar da zaune tsaye a lokacin bikin sallar babba, a don haka ne ma ya sanya suka dauki wadannan matakan na samar da tsaro a birnin Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel