Mayakan Boko Haram sun kai harin kunar baki wake jahar Borno, 3 sun mutu

Mayakan Boko Haram sun kai harin kunar baki wake jahar Borno, 3 sun mutu

Wasu kananan yaran mata guda biyu yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a jahar Borno, inda suka kashe mutane guda uku, sa’annan suka raunata wasu mutane Takwas, inji rahoton jaridar Guardian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Borno, SEMA, Bello Danbatta ya bayyana cewa yan kunar bakin wajen sun kai harin ne da yammacin Talata da misalin karfe 8:30 na dare a yankin Mafa.

KU KARANTA: Karanta wasu bayanai 8 masu muhimmanci game da aikin Hajji da Ka’aba

“Yan kunar bakin waken sun shiga garin Mafa ne tare da ayarin wasu Mata da suka fita karyo itacen girki, a daidai wannan lokaci ne suka tayar da bamabaman.” Inji Danbatta.

Boko Haram sun dade kusan shekara 10 kenan suna yaki da gwamnatin Najeriya da nufin kafa daular Musulunci a Najeriya, kuma suna amfani da kananan yara musamman mata wajen kai harin kunar bakin wake a masallatai, kasuwanni, gidajen kallo, teburin mai shayi, da kuma tashoshin mota.

Harin kunar bakin wake da suka kai a baya bayan nan shine wanda suka kai a watan Yuni a wani gidan kallon kwallo inda akalla mutane 30 suka mutu.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan saman Najeriya ta shigo da wasu kwararrun karnuka na musamman guda 21 daga kasar Afirka ta kudu wadanda suka samu horo a kan harkar binciko duk inda aka binne bamabamai, don habbaka yakin da take yi da yan ta’addan Boko Haram.

Haka zalika rundunar ta horas da wasu jami’anta guda 20, wadanda suka samu horo na tsawo makonni 13 a kan yadda zasu yi aiki tare da karnuna, wadanda ake kira ‘K-9’, su kuma Sojojin ake kiransu ‘K-9 handlers’.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel