Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kogi ta fara shirin tsige mataimakin gwamna

Yanzu Yanzu: Majalisar dokokin jihar Kogi ta fara shirin tsige mataimakin gwamna

- Majalisar dokokin jihar Kogi, ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Elder Simon Achuba

- Yan majalisar sun jingina kararsu akan laifuka uku da suka hada da ta’addanci, wawure dukiya da kuma rashin kokari

- Shugaban masu rinjayen ya tabbatar da cewa yan majalisar 21 cikin 25 sun sanya hannu a korafin

Majalisar dokokin jihar Kogi, a ranar Laraba, 7 ga watan Agusta, ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Elder Simon Achuba.

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Abdullahi Bello (Ajaokuta, APC) ne ya karanto takardar sanar da tsigewar a matsayin kara a zauren majalisar dokokin.

Yan majalisar sun jingina kararsu akan laifuka uku da suka hada da ta’addanci, wawure dukiya da kuma rashin kokari, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shugaban masu rinjayen wanda ya tabbatar da cewa yan majalisar 21 cikin 25 sun sanya hannu a korafin yace zarge-zarge, ayyuka da kuma kalaman mataimakin gwamnan sun saba ma ka’ida.

KU KARANTA KUMA: Yadda nayi rayuwa tsawon shekara 2 tare da yan ta’addan Boko Haram – Wani bawan Allah

Ya yi nuni ga sashi na 188 na kundin tsarin mulkin 1999 da kuma rokon majalisa na fara bincike gabannin yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

Kakakin majalisar, Kolawole Mathew ya amince da rokon da ke cikin karar sannan ya nemi a mika wa mataimakin gwamnan takardar karar domin jin martaninsa cikin kwanaki 14 kamar yadda doka ta tanadar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel