Toh fah: An garkame gidajen man fetur guda 53 a Kaduna

Toh fah: An garkame gidajen man fetur guda 53 a Kaduna

Rahotanni sun kawo cewa hukumar da ke kula da saida man fetur ta kasa (DPR), reshen jihar Kaduna, ta rufe gidajen sayar da man fetur da gas har guda 56 a cikin birnin jihar.

DPR ta bayyana cewa ta kulle gidajen man ne sakamakon kin bin ka’idojin da suka shafisayar da fetur a gas a fadin duniyar nan.

Shugaban hukumar na jihar, Isa Tafida ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zagayen gani-da-ido a kan gidajen mai na watan Yuli a jihar Kaduna.

Ya ce sun gudanar da samamen kulle gidajen mai din ne domin zakulo masu boye mai da masu karkatar da shi da kuma masu saidawa sama da adadin da aka kayyade farashin kowace lita.

Ya kara da cewa sun ziyarci gidajen mai 354 a fadin Jihar Kaduna inda suka samu ana saida lita daya kasa da Naira 143 zuwa 145 ka’idar da aka yanke wa lita daya.

Tafida ya kasa da cewa an ziyarci gidajen saida gas har guda 19.

KU KARANTA KUMA: Yadda nayi rayuwa tsawon shekara 2 tare da yan ta’addan Boko Haram – Wani bawan Allah

“An kulle gidajen mai 53, 11 daga cikin su saboda kin sayar da mai ana karkatar da shi, 40 saboda kin bin ka’idar dokar saida man fetur da rashin kiyaye ka’idar lafiya da rayuka da kiyaye dukiyoyi da sauran su.”

Ya gargadi masu saida mai su guji jefa kan su da gidajen man su cikin hada-hadar hakalla.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel