Yadda nayi rayuwa tsawon shekara 2 tare da yan ta’addan Boko Haram – Wani bawan Allah

Yadda nayi rayuwa tsawon shekara 2 tare da yan ta’addan Boko Haram – Wani bawan Allah

Wani bawan Allah ya bayar da labarin irin rayuwar da yayi bayan ya tsinci kansa a cikin yan ta’addan Boko Haram a lokacin da suka kaddamar da hari a garin Gwoza da ke jihar Borno.

Ya bayyana cewa sun yi rayuwa cikin kangi da bautawa yan ta’addan ta hanyar yi masu noman abinci bayan sun tafi da su zuwa wani waje, sakamakon harin da sojoji suka kaddamar akan yan ta’addan.

A cikin wannan yanayi ne har suka samu suka tsere cikin wani dare.

Ga yadda cikakken labarin yake: “Ina a Gwoza lokacin da aka kai hari garin. Mutane da dama sun tsere. Da dama sun tsere zuwa saman duwatsu. Amma yan ta’addan suka bi mu sannan suka tattauna damu game da addininsu. Muka ce bamu fahimci kashe-kashen da ke tattare da manufarsu ba. Amma duk da haka suka tursasa mana rayuwa dasu sannan suka dauke mu zuwa daji ayan harin sojoji akan su.

“Sojojin sun kai ma yan ta’addan hari sosai. Don haka Boko Haram suka dauke mu zuwa wani wuri sannan suka ajiye mu a wajen domin yin noma. Suna daukan abincin domin tanadin kansu.

“Suna bin gida-gida suna karban kayayyaki. Mun yi zama a haka har tsawon shekara biyu; suna mana barazana da kuma kashe wasu da dama. Sai muka shiga wani hali da kuma tsorata, don haka muka yanke shawarar tserewa cikin dare.

KU KARANTA KUMA: El-Zakzaky: Ina fatan za a cika sauran umurnin kotu - Falana

“Mun hadu da sojoji a kauyen da ke makwabtaka. An dauke mu zuwa kurkuku saboda basu tabbatar da ko mu yan ta’adda bane. Sojoji na taka-tsan-tsan da mutanen da suka yi zama da yan ta’adda; sai anyi maka tambayoyi da binike kafin a tura ka wajen sauya mutane. Na shafe shekaru biyu wajen horar da hallaya. Yanzu na dawo sansani dauke da sana’o’i amma babu aiki ko kudin fara sana’a."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel