El-Zakzaky: Ina fatan za a cika sauran umurnin kotu - Falana

El-Zakzaky: Ina fatan za a cika sauran umurnin kotu - Falana

Babban lauya da ke kare hakkin bil adama, Femi Falana ya yabi hukuncin babban kotun jihar Kaduna da ta yi umurnin sakin shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat don samun kulawar likitoci.

Mista Falana wanda ya kasance bako a shirin Channels Television na Sunrise Daily, yace basu damar zuwa yin magani a kasar waje ya ceto kasar daga tashin hankali mai tsanani.

Yace, “Na yi farin ciki a daren jiya da naji cewa hukumar tsaro na sirri (DSS) ta ba da sanarwa kan cewa zata bi umurnin kotu, sanna ina ganin cewa hakan wani ci gaba ne mai kyau”.

Babban lauyan kasar har ila yau yayi kira ga sakin sauran mutanen da aka rufe cikin gaggawa.

“Ina fatan cewa za a bi sauran umurnin kotun ciki harda na Dasuki saboda mu samu shiga jerin sauran kasashen da suka waye”.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sammaci Oshiomhole da manyan APC zuwa taron gaggawa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Femi Falana (SAN) a ranar Talata ya ce Shugaba Muhammadu Buhari na kokarin mayar da Najeriya baya zuwa lokacin da babu ‘yanci, saboda yinkurinsa na dakile zanga-zangar lumana wadda dokar kasa ta hana ba.

Falana yayi wannan furucin a cikin wata hirar talabijin da akayi da shi a Abuja, inda yake cewa: “ Lokaci na karshe da muka ga irin wannan abu shi ne a shekarar 1948, yayin da kungiyar Zikist ta soma irin wannan zanga-zangar ta juyin juya hali."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel