Buhari ya sammaci Oshiomhole da manyan APC zuwa taron gaggawa

Buhari ya sammaci Oshiomhole da manyan APC zuwa taron gaggawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar zuwa wani taron gaggawa a Aso Rock, Abuja.

A cewat jaridar The Nation, daga cikin ajandar taron, za a duba sakamakon zaben 2019 sannan a dauki matakan da suka kamata domin ci gaban jam’iyyar mai mulki.

An tattaro cewa taron zai tabbatar da cewar duk wadanda ke rike da mukami a karkashin inuwar jam’iyyar sun shiga cikin matakin Next Level na Shugaban kasa Buhari.

Har ila yau wasu na ganin cewa ganawar zai kuma shirya yan takarar APC gabannin zaben gwamnonin jihohin Bayelsa da Kogi mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi gaggawan sakin dukkanin yan siyasan da aka garkame – PDP tayi gargadi

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana ire-iren mabanbantan mutanen da a ka tara a matsayin abin da ya sa shugabancin kasar nan ya ke da wahala.

Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya shugabanci kasar a lokacin mulkin soji, ya nuna cewa banbancin mutanen da a ke da su a Najeriya ya na da amfani domin samun ra’ayoyi daban-daban.

Babangida wanda a ka fi sani da IBB ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai wahalar shugabanci ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel