Buhari yayi gaggawan sakin dukkanin yan siyasan da aka garkame – PDP tayi gargadi

Buhari yayi gaggawan sakin dukkanin yan siyasan da aka garkame – PDP tayi gargadi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi umurni domin a saki furusonin siyasa a kasar.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Mista Uche Secondus ne yayi kiran a ranar Talata, 6 ga watan Agusta, a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Mista Secondus wanda ya kai ziyarar jaje ga Gwamna Umaru Fintiri akan rashin mahaifinsa da yayi, ya yi Allah wadai da kama mutane, hade da kamun Mista Omoleye Sowore.

A cewar Shugaban jam’iyyar na PDP, wannan ne karo na farko da gwamnatin damokardiyya ke garkame yan siyasa sannan kuma ta ki sakin su.

Ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki, inda ya karfafa cewa wannan yana iya janyo tangarda a zaman lafiyan kasar.

Sowore, mai wallafa labarai a sashin yanar gizo na Sahara Reporters ya shiga hannun jami’an tsaro na farin kaya a ranar Asabar a jihar Legas.

An rahoto cewa kama shi na da dangantaka da zanga-zangar “RevolutionNow” wanda aka shirya gudanarwa a fadin kasar a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda Buhari ya nuna alhini kan mutuwar daliban ATBU bayan rufatawar gada

Gabannin zanga zangan, yan sanda sun gargadi masu shiryawa da kuma mambobi dasu janye shirinsu da kuma kaurace ma duk wani mataki da zai sa su amshe gwamnati ta karfi da yaji.

Ko da yake ba ayi nasaran kaddamar da zanga zangar ba kamar yanda aka shirya a wasu jihohin, masu zanga zanga wadanda suka ki daukan gargadin yan sandan sun shiga hannu a yankin Surulere a Legas.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel