Mahajjatan Najeriya 65,000 na Saudiyya yanzu - NAHCON

Mahajjatan Najeriya 65,000 na Saudiyya yanzu - NAHCON

Hukumar jin dadin alhazan Najeriya (NAHCON) a ranar Talata ta bayyana cewa akalla mahajjatan Najeriya 65,000 na kasar Saudiyya a yanzu domin aikata ibadan aikin Hajjin bana.

Wani jami'in hukumar, Dakta Aliyu Tanko, ya bayyanawa manema labarai a Makkah cewa an yi shirye-shiryen da ya kamata domin saukakawa mahajjata ibadan da za'a fara ranar Asabar.

Ya ce dukkan maniyyatan Najeriya sun isa kasa mai tsarki kuma suna gabatar da ibadu daban-daban gabanin aikin hajji.

Hukumomin kasar Saudiya sun yi wa Najeriya tanadin kujerun maniyyata 95,000 a bana. A yayin da jihohin Najeriya suka kasafta guraben kujerun maniyyata 65,000 karkashin kulawa ta hukumar jin dadin Alhazai, masu bibiyar jirgin yawo sun ribaci sauran kujerun 30,000.

KU KARANTA: Tafiya Indiya jinya: Ana shiryawa Zakzaky da matarsa sabon fasfot

NAHCON ta ce jirgi mai lamba Flynas XY5821, ya yi dakon sahun karshe na maniyyatan Najeriya 301 da kuma ma'aikata 19 bayan barin garin Abuja inda kuma ya isa filin jirgin saman birnin Jedda na kasar Saudiya da misalin karfe 8.53 na safiyar Litinin.

Jirgi cikon na 93 da ya yi jigila ta karshe a ranar Litinin, ya yi dakon maniyyatan Abuja, Sakkwato, Zamfara, Kaduna, Anambra, Abia, Kuros Riba, Delta, Ebonyi da kuma Enugu. Ya kasance jirgi da ya yi dakon rukunin karshe na maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiya a bana.

Jihohi 32 na Najeriya da maniyyatansu suka daura haramar gudanar da aikin hajji a bana sun hadar da Filato, Jigawa, Borno, Legas, Bauchi, Taraba, Yobe, Oyo, Osun, Ogun, Gombe, Katsina, Kano, Kaduna, Nasarawa, Kebbi, Kwara, Kogi, Sakkwato, Adamawa, Neja, Edo, Ekiti, Ondo, Zamfara, Anambra, Abia, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Enugu da kuma birnin Tarayya Abuja.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel