Ni ne nan jagoran ‘inconclusive’ – Ganduje

Ni ne nan jagoran ‘inconclusive’ – Ganduje

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yiwa 'yan wasan Kano Pillars wata babbar kyauta

-Gwamnan jihar Kano ya bayyana kansa da kungiyar kwallon kafan a matsayin jagororin 'inconclusive' bayan da kungiyar ta doke Niger Tornadoes a zagayen bugun daga kai sai mai tsaron gida

-Kakakin gwamnan jihar Abba Anwar ya ce akwai liyafa da aka shiryawa kungiyar domin basu karramawa ta musamman

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje cikin wasa ya bayyana kansa a matsayin jagoran ‘inconclusive’ bisa la’akari da nasarar da ya samu ta lashe zaben gwamnan Kano wanda akayi a shekarar nan.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Ganduje shi ne yayi nasarar lashe zaben gwamnan Kano wanda aka sake yi a ranar 23 ga watan Maris bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta sanar cewa zaben 11 ga watan Maris kammalu ba.

KU KARANTA:Zanga-zangar juyin juya hali: Buhari na kokarin mai damu baya zuwa 1948 – Falana

Gwamnan yayi wannan jawabin ne ranar Litinin a lokacin da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars (Sai masu gida) suka kawo masa sabon kofin da suka lashe kwanan ofishinsa.

Kano Pillars ce ta lashe kofin Aiteo Cup kwanan a Kaduna, inda ta karya tarihin shekara 66 da tayi ba tare da lashen kofin ba. Kano Pillars din ta doke takwararta ne ta Niger Tornadoes 4-3 a lokacin da wasan ya kai zagayen bugun da kai sai mai tsaron gida.

“ Na riga da nasan Kano Pillars za ta lashe wasan tunda naga ya kai fagen matakin ‘inconclusive’,” inji gwamnan ya fadi yana dariya.

“ A matsayinmu na jagororin inconclusive, a karon karshe sai ga shi munyi nasarar lashe kofin. Wannan kuma nasarar ta samu ne a dalilin hazikan ‘yan wasan da muke dasu.” Inji Ganduje.

Har ila yau, gwamnan ya bi ‘yan kwallon da kyautar daloli inda ko wannensu ya tashi da $1000 wanda yayi daidai da N360,000 a kudin Najeriya a matsayin tukwicin lashe Aiteo cup.

Gwamnan a wani zance da kakakins Abba Anwar ya fitar ya ce, akwai karramawa ta musamman da za a yiwa kungiyar a wata liyafar da za a shirya masu kwanan nan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel