Kotu za ta saurari karar DSS na tsare Sowore a gobe Alhamis

Kotu za ta saurari karar DSS na tsare Sowore a gobe Alhamis

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 8 ga watan Agusta, domin yanke hukunci akan karar da hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta shigar na tsare jagoran zanga-zangar juyin juya hali, Omoyele Sowore na tsawon kwanaki 90, zuwa lokacin kammala bincikenta.

Justis Taiwo Taiwo a ranar Talata, 6 ga watan Agusta ya dage karar domin bashi damar kallon faiffan bidiyon da hukumar DSS ta sanya cikin karar nata.

Da farko dai, lauyan DSS, G. O. Abadua yace an shigar da karar ne domin nem tsare Sowore na sama da sa’o’i 48 da doka ta bayar biyo bayan kamunsa.

Jami’an DSS ne suka kama Sowore, wanda ya kasance mawallafin jaridar Sahara Reporters kumadan takarar shugan kasa a jam’iyyar African Action Congress (AAC), a zaben 2019 a ranar Aabar a Lagas.

Hukumar tsaron tace an kama Sowore bisa ga kokari jan ramar zanga-zangar juyin juya hali n agama gari akan gazawar gwamnatin kasar.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda Buhari ya nuna alhini kan mutuwar daliban ATBU bayan rufatawar gada

A safiyar ranar Lahadi kuma sai aka mayar da Sowore babbar birnin tarayya, Abuja sannan a yanzu haka yana tsare a hannun DSS.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Tsohon shugaban jam’iyyar People’s Redemption Party, Alhaji Balarabe Musa yayi Allah wadai da kamun tsohon dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore akan jagorantar zanga-zangar juyin juya hali akan gwamnatin kasar.

A wata hira da manema labarai a Kaduna, Musa yace al’umman kasar na da ikon yin zanga-zanga a inda gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da shugabanci na gari, kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu yanci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel