Kisan 'yan Najeriya: Buhari zai gana da shugaban kasar Afirka ta Kudu

Kisan 'yan Najeriya: Buhari zai gana da shugaban kasar Afirka ta Kudu

Domin gano bakin zare tare da magance ta'addancin da ake zartarwa kan 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai gana da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramahosa.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugaba ta hukumar kula da harkokin waje da 'yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM), Honarabul Abike Dabiri-Erewa, yayin da ta ke zantawa da manema labarai a ranar Laraba cikin birnin Abuja.

Baya ga tattaunawa a kan sha'anin ta'addanci na kyamatar 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu da za ta gudana a birnin Tarayya, shugabannin biyu za kuma su gana da juna domin tumke damarar dangartakar kasashen su.

Yayin jaddada cewar ta'addancin kyamatar 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu ya kai intaha, Honarabul Dabiri ta ce ya kamata a dauki tsauraran matakai da za su magance wannan mugun nufi da kuma dakile ta'azzararsa.

A cewarta, ministan kula da karkokin kasashen ketare na Najeriya da kuma na kasar Afirka ta Kudu za su gana da juna a kan wannan lamari da zarar shugaban Buhari ya rantsar da majalisar ta zantarwa a ranar 21 ga watan Agusta.

Ta ce za su ci gaba da tumke damarar kyakkyawar dangartakar da ke tsakanin kasashen biyu domin magance wannan mummunar barazana mai haddasa ta'addanci na kyamatar 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu.

KARANTA KUMA: Hajjin Bana: Bamu karbi kudin hadayar maniyyatan Kano ba - Hukumar Alhazai

Daga shekarar 2018 kawowa yanzu, Misis Dabiri ta ce an kashe 'yan Najeriya 88 a kasar Afirka ta Kudu.

A wata wallafar jaridar BBC Hausa ta ranar 7 ga watan Fabrairun 2017, shugabar hukumar NIDCOM ta ce a tsakanin shekarar 2016 da kuma 2017, an kashe 'yan Najeriya 116 a kasar Afirka ta Kudu ba bisa ka'ida. Ta kuma zargi 'yan sandan kasar da wannan aika-aika.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel