Gwamnatin Kaduna ta nemi haramtawa Zakzaky izinin tafiya kasar Indiya

Gwamnatin Kaduna ta nemi haramtawa Zakzaky izinin tafiya kasar Indiya

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana shirinta na neman daukaka kara dangane da hukuncin da babbar kotun jihar ta zartar a ranar Litinin, wadda ta bai wa shugaban mabiya akidar shi'a Sheikh Ibrahim Zakzaky izinin tafiya kasar Indiya domin neman lafiya.

Babban jami'in hukumar gurfanarwa na jihar Kaduna, Mista Dari Bayero, shi ne ya bayar da tabbacin hakan cikin wata sanarwa da ya gabatar wa manema labarai na jaridar The Punch a ranar Talata.

Yunkurin gwamnatin na zuwa ne bayan da hukumar 'yan sandan fararen kaya DSS, ta sha alwashin yi wa umarnin babbar kotun jihar biyayya wadda ta bayar da izinin tafiya kasar Indiya ga Zakzaky da ke tsare a hannunta tun a shekarar 2015.

Bayero ya ce gwamntin Kaduna za ta daukaka kara domin kalubalantar hukuncin da babbar kotun ta zartar tare da sharudan da ta gindaya na bai wa Zakzaky izinin tafiya kasar Indiya wajen neman lafiya.

Sai dai lauya mai kare hakkin dan Adam wanda ya wakilci Zakzaky a gaban kotu, Femi Falana (SAN), ya ce ba ya da masaniyar wani sharadi da kotun ta gindaya yayin zartar da hukuncin bai wa Zakzaky damar fita jinya.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda ya shimfidawa masu Adaidaita Sahu dokoki a jihar Kano

Legit.ng ta fahimci cewa, jagoran kungiyar IMN wadda aka fi sani da Shi'a, Sheikh Zakzaky, ya shiga hannun hukumar DSS tare da mai dakinsa Zeenatu tun a shekarar 2015 bayan wata takaddama da auku tsakaninsa da shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai a birnin Zazzau na garin Zaria.

A safiyar ranar Litinin ne dai babbar kotun jihar Kaduna ta ba jagoran mabiya mazhabar Shi'a Zakzaky da mai dakinsa damar fita nema magani a birnin New Delhi na kasar Indiya kamar yadda lauyoyinsa suka nema.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel