Hukumar 'yan sanda ta shimfidawa masu Adaidaita Sahu dokoki a jihar Kano

Hukumar 'yan sanda ta shimfidawa masu Adaidaita Sahu dokoki a jihar Kano

A ranar Talata 6 ga watan Agustan 2019, hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta murtuke fuska a kan matuka babura masu kafa uku wanda aka fi sani da 'yan Adaidaita Sahu, da su tabbatar da kiyaye dokokin tituna da kuma yi masu da'a.

Hukumar 'yan sandan ta yi zargin cewa matuka babura masu kafa uku na da babban alhaki wajen haifar da hatsarurruka da muzgunawa masu sauran ababen hawa a kan hanyoyi babu gaira babu dalili.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan Kano Abdullahi Haruna ya shaidawa manema labarai, ya ce dole ne 'yan Adaidaita Sahu su kasance sun mallaki rajistar ababen su na hawa da kuma lambar hukumar KAROTA manne a jikin baburansu.

Sanarwar da babban jami'in 'yan sandan ya gabatar ya ce wannan hukunci da aka zartar ba ya da wata manufa face tabbatar da tsare rayuka da kuma dukiyoyin al'ummar jihar Kano.

KARANTA KUMA: Rauni: Babu Messi kungiyar Barcelona za ta buga wasan farko a kakar La Liga ta bana

Hukumar 'yan sandan ta ce za ta dauki tsauraran matakai a kan 'yan Adaidaita Sahu masu daukar fasinjoji da suka wuce ka'ida da kuma goyon fasinjoji a gefen baburansu. Kazalika hukumar za ta hukunta duk wanda aka samu ba tare da lambar rajista ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel