Gwamnati bata da ikon kama Sowore – Balarabe Musa

Gwamnati bata da ikon kama Sowore – Balarabe Musa

Tsohon shugaban jam’iyyar People’s Redemption Party, Alhaji Balarabe Musa yayi Allah wadai da kamun tsohon dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore akan jagorantar zanga-zangar juyin juya hali akan gwamnatin kasar.

A wata hira da manema labarai a Kaduna, Musa yace al’umman kasar na da ikon yin zanga-zanga a inda gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da shugabanci na gari, kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu yanci.

“Gwamnati bata da yancin kama Sowore don ya jagoranci zanga-zanga ko ya soki gwamnatin Buhari. Yunkurinsa ba cin amanar kasa bane. Ba za ka iya kama kowani dan Najeriya da yayi zanga-zangar adawa da gwamnatin Buhari ba.

KU KARANTA KUMA: Mabanbanatan mutanen da a ke da su ya sa mulki ya ke da wahala – IBB

“Halin da kasar take ciki ya munana sosai. Yan Najeriya sun yi hakuri da yawa. Akwai bukatar yin zaga-zanga akan yanayin shugabancin Buhari. Don haka, muna da yancin yin zanga-zanga. Sannan sauyin da mutane ke kira ga a wannan kasar ba cin amanar kasa bane. Don haka wadanda ke kan mulki su kwana da sanin cewa yan Najeriya ba za su iya jure wannan rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki ba. Ya zama dole ayi abunda ya kamata domin ceto Najeriya,” inji shi.

Alhaji Musa ya kuma bayyana cewa gwamnatin Buhari na da iyaka da kundin tsarin mulki ta bata na tsare abokan hammayar siyasarsa da sunan dalilai na tsaro.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel