Zulum ya bada umarni a biya Ma’aikata fansho da kudin alawus na hutu

Zulum ya bada umarni a biya Ma’aikata fansho da kudin alawus na hutu

- Gwamnan Jihar Borno ya sa hannu domin biyan fansho da alawus din wasu Ma’aikata

- Akalla Ma’aikata 10, 300 za su amfana da wadannan tarin kudi da za a fitar a jihar Borno

- Ma’aikata 9, 898 za su samu kudin hutu, yayin da za a biya Iyalin wasu kudin sallama

Mun samu labari cewa mai girma gwamna Babagana Umara Zulum ya bada umarni a biya ma’aikatan gwamnatin jihar Borno dukannin kudin hutunsu da su ka makale a shekarar 2018.

Ma’aikata 9, 898 za su samu wannan kudi a matsayin alawus din su na tafiya hutun aiki kamar yadda mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai watau Isa Gusau ya bayyana a jiya.

A Ranar Talata, 7 ga Watan Agusta, 2019, Malam Isa Gusau ya fitar da jawabi cewa gwamna ya ba shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar da ma’aikatar kudi ta Borno umarni su biya wannan kudi.

KU KARANTA: Rikicin gida ya rutsa da PDP a Jihar Bayelsa a na shirin zaben tsaida gwani

Daga cikin wadanda za su amfana da wannan kudi akwai Iyalai 185 na ma’aikatan da su ka rasu. Haka zalika za a biya Iyalai 236 wasu alawus a sakamakon rashin masu daukar nauyinsu.

Har wa yau gwamnatin Borno za ta bada alawus na musamman na sayen kayan aiki ga wasu manyan Sakatarorin din-din-din da gwamna ya iske a lokacin da ya kai wata ziyarar ba-zata.

Gwamnan ya cika alkawarin da ya dauka bayan ya hau mulki inda ya umarci hukumomin jihar su biya alawus din hutu na 2019 ga ma’aikata 96 da ya samu a ofis lokacin da ya kai ziyara a Mayu.

Wannan na zuwa ne bayan gwamna Babagana Zulum ya bada umarni a biya wasu tsofaffin ma’aikata 1, 600 da su ka yi ritaya daga aiki kudin sallamarsu da ya makale tun a shekarar 2013.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel