Za mu fitar da ke-ke-da-ke na asusun NNPC Inji Mele Kyari

Za mu fitar da ke-ke-da-ke na asusun NNPC Inji Mele Kyari

Labari ya zo mana cewa shugaban kamfanin man Najeriya na NNPC, Malam Mele Kyari Kolo, ya bayyana zai cika alkawarin da kamfanin ya yi na yin aiki da gaskiya ba tare da wuru-wuru ba.

Mele Kolo Kyari ya nuna cewa kwanan nan NNPC za su fitar da diddikin rahoton akawun dinsu. Shugaban kamfanin man ya bayyana wannan ne lokacin da hukumar NEITI ta kai masa wata ziyara.

Mista Waziri Adio ya tashi kafa-ya-kafa har ofishin shugaban na NNPC da ke babban birnin tarayya Abuja, a Ranar Talata 7 ga Watan Agusta, 2019, kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust.

Malam Kyari ya fadawa Sakataren na NEITI mai kokarin ganin an yi gaskiya a harkokin man Najeriya, cewa za su fitar da rahoton kudin da su ka batar, abin da an yi shekara da shekaru NNPC ba su yi ba.

KU KARANTA: Za a yi wa yadda a ke rabon dukiyar kasa garambawul a Najeriya

Sai dai kuma duk da shirin da NNPC ke yi na wallafa binciken da a ka yi wa asusunsu, Mele Kyari ya nuna cewa ba za su bari wasu su fake da neman bayanai wajen jefa kamfanin cikin rikicin siyasa ba.

Kyari ya ce: “Ku na sane cewa a wasu lokuta a kan samu mutane masu makarkashiya da ke fakewa a karkashin inuwar FOI wajen cin ma manufar siyasarsu. NNPC na samun wahala da irin wannan.”

Shugaban kamfanin na NNPC ya cigaba da yin karin haske da cewa: “Mu na bi a hankali domin burmawa rikicin siyasa ko kuma batawa wasu.” Kakakin NNPC, Ndu Ughamadu, ya fitar da wannan jawabi.

Dokar FOI ta ba mutanen kasa damar samun duk wani bayanai daga kamfani, hukuma ko ma’aikatar gwamnati. A na sa bangaren, Waziri Adio, ya yabawa kokarin da NNPC ke yi a yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel